Irmiya 29:2 - Littafi Mai Tsarki2 (Ya rubuta wannan bayan tashin sarki Yekoniya, da uwa tasa, da bābāni, da sarakunan Yahuza, da na Urushalima, da gwanayen aikin hannu, da maƙera daga Urushalima.) အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 (Wannan ya faru bayan Sarki Yekoniya da mahaifiyar sarauniya, shugabannin fada da kuma dukan shugabannin Yahuda da Urushalima, gwanayen sana’a da masu sassaƙa suka tafi zaman bauta daga Urushalima.) အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kama Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, daga Urushalima, ya kai shi bautar talala a Babila, tare da sarakunan Yahuza, da gwanayen sana'a, da maƙera, dukansu, ya kawo su Babila. Sai Ubangiji ya nuna mini wannan wahayi. Na ga kwando biyu na ɓaure, an ajiye su a gaban Haikalin Ubangiji.