Kowane irin aiki da ya kama na hidimar Haikalin Allah, wanda yake kuma bisa ga doka da umarni, na neman Allahnsa, ya yi su da zuciya ɗaya, ya kuwa arzuta.
Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa'ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama suka ce, “Shi jikan Yehoshafat ne wanda ya nemi Ubangiji da zuciya ɗaya.” Don haka a gidan Ahaziya ba wanda ya isa ya riƙe mulkin.
Sarki ya tsaya kusa da ginshiƙi ya yi alkawari ga Ubangiji, cewa zai bi Ubangiji da zuciya ɗaya, da dukan ransa. Zai kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa, ya bi maganar alkawarin da aka rubuta a littafin. Dukan jama'a kuma suka yi alkawarin.
domin Ubangiji ya cika maganar da ya faɗa mini cewa, ‘Idan 'ya'yanka suna lura da hanyarsu, sun yi tafiya a gabana da gaskiya da zuciya ɗaya, da dukan ransu, ba za ka rasa mutum wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba.’
Yanzu fa sai ku sa hankalinku da zuciyarku ga neman Ubangiji Allahnku. Ku tashi, ku gina wa Ubangiji Allah tsattsarkan wuri domin a kawo akwatin alkawari na Ubangiji, da tsarkakakkun tasoshin Allah a cikin Haikalin da aka gina saboda sunan Ubangiji.”
“Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.
Ba a ɓoye na yi magana ba, Ban kuwa ɓoye nufina ba. Ban ce jama'ar Isra'ila Su neme ni a kowace hanyar ruɗami ba. Ni ne Ubangiji, gaskiya kuwa nake faɗa, Ina sanar da abin da yake daidai.”