Amma maganata da dokokina waɗanda na umarta wa bayina annabawa, sun tabbata a kan kakanninku, sai suka tuba, suka ce, ‘Kamar yadda Ubangiji Mai Runduna ya yi niyya ya yi da mu saboda hanyoyinmu da ayyukanmu, haka kuwa ya yi da mu.’ ”
Ya zama fa a wannan shekara, a watan biyar, a shekara ta huɗu ta sarautar Zadakiya Sarkin Yahuza, sai annabi Hananiya ɗan Azzur mutumin Gibeyon, ya yi magana da ni a Haikalin Ubangiji, a gaban firistoci da dukan jama'a, ya ce,
Ga maganar wasiƙar da annabi Irmiya ya aika daga Urushalima zuwa ga dattawa, da firistoci, da annabawa, da dukan mutanen da Nebukadnezzar ya kwaso daga Urushalima zuwa Babila.