Irmiya 27:6 - Littafi Mai Tsarki6 Yanzu fa na ba bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila, dukan ƙasashen nan, na kuma ba shi namomin jeji su bauta masa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Yanzu zan ba da dukan ƙasashenku ga bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon; zan sa namun jeji ma su bauta masa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kama Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, daga Urushalima, ya kai shi bautar talala a Babila, tare da sarakunan Yahuza, da gwanayen sana'a, da maƙera, dukansu, ya kawo su Babila. Sai Ubangiji ya nuna mini wannan wahayi. Na ga kwando biyu na ɓaure, an ajiye su a gaban Haikalin Ubangiji.
Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’