Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 27:20 - Littafi Mai Tsarki

20 wato waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila bai kwashe ba a lokacin da ya tafi da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, da dukan dattawan Yahuza da na Urushalima zuwa bauta a Babila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe sa’ad da ya kame Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon tare da dukan manyan mutanen Yahuda da Urushalima,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 27:20
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Bayan da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kama Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, daga Urushalima, ya kai shi bautar talala a Babila, tare da sarakunan Yahuza, da gwanayen sana'a, da maƙera, dukansu, ya kawo su Babila. Sai Ubangiji ya nuna mini wannan wahayi. Na ga kwando biyu na ɓaure, an ajiye su a gaban Haikalin Ubangiji.


Da bazara sai sarki Nebukadnezzar ya aika aka kawo shi Babila tare da kayayyaki masu daraja na Haikalin Ubangiji. Ya kuma naɗa Zadakiya ɗan'uwan Yekoniya ya zama Sarkin Yahuza da Urushalima.


Ashe, Yekoniya kamar fasasshen tulu yake, Wanda ba wanda ya kula da shi? Me ya sa aka watsar da shi da 'ya'yansa, A ƙasar da ba su sani ba?


Ya kwaso dukan kayayyakin da suke a Haikalin Allah, manya da ƙanana, da dukiyar da take a Haikalin Allah, da ta sarki, da ta sarakunansa ya kai su Babila.


Yosiya ya haifi Yekoniya da 'yan'uwansa, wato, a lokacin da aka ɗebe su zuwa Babila.


Bayan an ɗebe su zuwa Babila, sai Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Shayeltiyel ya haifi Zarubabel,


Wato, dukkan zuriya daga Ibrahim zuwa kan Dawuda, zuriya goma sha huɗu ce. Daga Dawuda zuwa ga ɗebe su a kai Babila kuwa, zuriya goma sha huɗu. Daga ɗebe su zuwa Babila zuwa kan Almasihu, zuriya goma sha huɗu.


Sai Yekoniya Sarkin Yahuza ya ba da kansa ga Sarkin Babila shi da tsohuwarsa, da fādawansa da hakimansa. Sarkin Babila ya kama shi yana da shekara takwas da sarautar,


Ba sarkin da zai yi mulkin ƙasar, dukan shugabanni kuma za su ƙare.


“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa a kan kayayyakin da suka ragu a Haikalin Ubangiji, da a fādar Sarkin Yahuza, da a Urushalima,


(Ya rubuta wannan bayan tashin sarki Yekoniya, da uwa tasa, da bābāni, da sarakunan Yahuza, da na Urushalima, da gwanayen aikin hannu, da maƙera daga Urushalima.)


A lokacin da Yehoyakim, ɗan Yosiya yake mulkin Yahuza, sai Ubangiji ya ce wa Irmiya,


Ubangiji kuwa ya ba Nebukadnezzar nasara a kan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, sai ya kwashe waɗansu kayayyakin Haikalin Allah, ya kawo su ƙasar Shinar a gidan gunkinsu, ya ajiye kayayyakin a baitulmalin gunkinsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ