Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 27:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Gama Ubangiji Mai Runduna ya faɗi zancen ginshiƙai, da babbar kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da ginshiƙai, kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 27:19
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Kaldiyawa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalansu, da kwatarniyar ruwa na tagullar da take cikin Haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagullar zuwa Babila.


Tsayin kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne. A kan kowane ginshiƙi akwai dajiyar tagulla, wadda tsayinta ya kai kamu uku. Akwai raga da rumman na tagulla kewaye da dajiyar.


Ubangiji kuwa ya ba Nebukadnezzar nasara a kan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, sai ya kwashe waɗansu kayayyakin Haikalin Allah, ya kawo su ƙasar Shinar a gidan gunkinsu, ya ajiye kayayyakin a baitulmalin gunkinsa.


Huram kuma ya yi kewayayyiyar babbar kwatarniya ta zubi da tagulla. Faɗinta kamu goma ne, tsayinta kuwa kamu biyar, da'irarta kuma kamu talatin ne.


Ya kuma yi dakali goma da tagulla. Kowane dakali tsawonsa kamu huɗu, faɗinsa kuma kamu huɗu, tsayinsa kuwa kamu uku ne.


Ya kwaso dukan kayayyakin da suke a Haikalin Allah, manya da ƙanana, da dukiyar da take a Haikalin Allah, da ta sarki, da ta sarakunansa ya kai su Babila.


Maƙiyi ya miƙa hannunsa A kan dukan kayanta masu daraja, Gama ta ga al'ummai sun shiga Haikali, Su waɗanda ka hana su shiga cikin jama'arka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ