Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 26:2 - Littafi Mai Tsarki

2 “Ka tsaya a filin Haikalin Ubangiji, ka yi wa dukan biranen Yahuza magana, su waɗanda suka zo Haikalin Ubangiji domin su yi sujada. Ka faɗa musu dukan maganar da na umarce ka, kada ka rage ko ɗaya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka tsaya a filin gidan Ubangiji ka kuma yi magana ga dukan mutanen garuruwan Yahuda waɗanda suka zo sujada a gidan Ubangiji. Ka faɗa musu kome da na umarce ka; kada ka bar wata magana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 26:2
32 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kada ku ƙara, ko ku rage kome daga cikin abin da na umarce ku, amma ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, waɗanda nake umartarku da su.


domin ban ji nauyin sanar da ku dukan nufin Allah ba.


kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”


Sa'an nan Irmiya ya komo daga Tofet, inda Ubangiji ya aike shi don ya yi annabci, sai ya tsaya a fili na Haikalin Ubangiji, ya ce wa dukan jama'a,


Amma kai, ka tashi ka sha ɗamara, ka faɗa musu dukan abin da na umarce ka. Kada ka ji tsoronsu domin kada in tsoratar da kai a gabansu.


Kun kuma san yadda ban ji nauyin sanar da ku kowane abu mai amfani ba, ina koya muku a sarari, da kuma gida gida,


Kowace rana kuwa, ko a Haikali ko a gida, ba su daina koyarwa da yin bishara, cewa Yesu shi ne Almasihu ba.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a bayyane, na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban faɗi kome a ɓoye ba.


Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, sai ka ji, ka karɓi dukan maganata da zan faɗa maka.


Sai Baruk ya karanta maganar Irmiya wadda take a takardar, kowa yana ji, a cikin Haikali a ɗakin Gemariya ɗan Shafan, magatakarda. Ɗakinsa yana a shirayi na bisa a hanyar shiga Sabuwar Ƙofa ta Haikalin Ubangiji.


Bari annabin da yake da mafarki ya faɗi mafarkinsa, amma wanda yake da maganata ya faɗe ta da aminci. Me ya haɗa ciyawa da alkama? Ni Ubangiji na faɗa.


“Ka tafi ka tsaya a ƙofar Haikalin Ubangiji, ka yi shelar wannan magana, ka ce, su kasa kunne ga maganar Ubangiji, dukansu mutanen Yahuza, su da suke shiga ta ƙofofin nan don su yi wa Ubangiji sujada!


“Ku lura, ku aikata dukan abin da na umarce ku da shi, kada ku ƙara, kada ku rage daga cikinsa.


In kuma wani ya yi ragi a maganar littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai, da na tsattsarkan birnin, waɗanda aka rubuta a littafin nan.


Sai wani ya zo ya ce musu, “Ai, ga shi, mutanen nan da kuka sa a kurkuku suna nan a tsaye a Haikali, suna koya wa jama'a.”


Da sassafe kuma ya sāke shiga Haikali. Duk mutane suka zo wurinsa, ya kuwa zauna yana koya musu.


Kowace rana ya yi ta koyarwa a Haikali. Amma manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama'a suka nema su hallaka shi.


Annabi Irmiya kuwa ya ce musu, “Na ji abin da kuka ce. Ga shi kuwa, zan yi addu'a ga Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka roƙa. Kowace irin amsa da Ubangiji ya bayar, zan faɗa muku, ba zan ɓoye muku kome ba.”


Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin kabilanku duka, inda zai sa sunansa, ya mai da shi wurin zamansa.


“Saboda haka za ka faɗa musu waɗannan abubuwa duka, amma ba za su ji ka ba. Za ka kira su, amma ba za su amsa ba.


“Yanzu fa, kai ɗan mutum, na sa ka zama ɗan tsaro a al'ummar Isra'ila. Duk lokacin da ka ji magana daga bakina, sai ka faɗakar da su.


Sai mutumin nan ya ce mini, “Ɗan mutum ka duba da idonka, ka ji da kunnuwanka, ka kuma mai da hankali ga dukan abin da zan nuna maka, gama saboda haka aka kawo ka nan. Sai ka sanar wa jama'ar Isra'ila abin da ka gani duka.”


Babu wata kalmar da Musa ya umarta, da Joshuwa bai karanta a gaban dukan taron Isra'ilawa ba, tare da mata da ƙanana, da baƙin da suke zaune tare da su.


Amma Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ce kai yaro ne, Kai dai ka tafi wurin mutanen da zan aike ka,


a shekarar ce, annabi Irmiya ya yi wa dukan mutanen Yahuza da dukan mazaunan Urushalima magana cewa,


Sa'an nan annabi Irmiya ya yi magana da annabi Hananiya a gaban firistoci da dukan jama'ar da suke tsaye a Haikalin Ubangiji, ya ce,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ