Irmiya 26:12 - Littafi Mai Tsarki12 Sa'an nan sai Irmiya ya yi magana da dukan sarakuna da dukan jama'a, ya ce, “Ubangiji ne ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan Haikali da wannan birni, da irin maganar da kuka ji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Sai Irmiya ya ce wa dukan fadawa da kuma dukan mutane, “Ubangiji ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan gida da wannan birni dukan abin da na faɗa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Idan sun tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Saboda labarin abin da yake zuwa. Sa'ad da ya zo, kowace zuciya za ta narke, hannuwa duka za su yi suwu, kowane ruhu kuma zai suma, gwiwoyi duka kuwa za su rasa ƙarfi kamar ruwa. Ga shi, abin yana zuwa, zai tabbata,’ ni Ubangiji Allah na faɗa.”