Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 25:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Duk da haka ba ku kasa kunne gare shi ba, shi Ubangiji ya faɗa, sai kuka tsokane shi da ayyukan hannuwanku. Wannan kuwa zai cuce ku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 “Amma ba ku saurare ni ba,” in ji Ubangiji, “kun tsokane ni da abin da kuka yi da hannuwanku, kuka kuma kawo lahani wa kanku.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 25:7
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

saboda sun aikata mugunta a gabana, suka tsokane ni in yi fushi tun ranar da kakanninsu suka fito daga Masar har wa yau.”


Mutumin da bai same ni ba ya cuci kansa, Duk wanda yake ƙina mutuwa yake ƙauna.”


Suka yi hadaya ta ƙonawa da 'ya'yansu mata da maza. Suka yi duba, suka yi sihiri, suka duƙufa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji, suka sa shi ya yi fushi.


Suka sa ni kishi da abin da ba Allah ba, Suka tsokani fushina da gumakansu, Ni kuma zan sa su su yi kishi da waɗanda suke ba mutane ba. Zan tsokane su da wawanyar al'umma.


“Amma suka yi maka rashin biyayya, suka tayar maka, Suka juya wa dokokinka baya, Suka karkashe anna bawan da suka faɗakar da su, Waɗanda suka faɗa musu su juyo gare ka. Suka yi ta saɓa maka lokaci lokaci.


“Domin haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Tun da yake kun ƙi yin biyayya da maganata,


Me ya sa kuke tsokanata da ayyukan hannuwanku, kuna miƙa wa gumaka hadayu a ƙasar Masar inda kuka zo don ku zauna? Yin haka zai sa a hallaka ku, ku zama abin la'ana da zargi a cikin dukan ƙasashen duniya.


Duk da haka Allah ya aika musu da annabawa don su komo da su wurinsa. Ko da yake sun shaida musu kuskurensu, duk da haka ba su kula ba.


“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ga shi, ina aukar wa wannan birni da dukan garuruwansa dukan masifu da na ambata a kansa, domin sun taurare zukatansu, sun ƙi jin maganata.’ ”


Ubangiji ya yi muku magana a lokacin wadatarku. Amma kun ce, “Ba za mu kasa kunne ba!” Wannan shi ne halinku tun kuna samari, Don ba ku yi biyayya da murya Ubangiji ba.


Domin ba su ji maganata wadda ni Ubangiji na faɗa ba, na yi ta aika muku da ita ta wurin bayina annabawa, amma kuka ƙi, ni Ubangiji na faɗa.


“Yanzu, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ina tambaya, me ya sa kuke jawo wa kanku wannan babbar masifa, kuna so ku hallakar da mata da maza, yara da jarirai daga cikin Yahuza, har a rasa wanda zai wanzu?


Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na dā suka yi ta yi musu shela suna cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, ku bar mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku.’ Amma ba su ji ba, ba su kuwa kula ba, ni Ubangiji na faɗa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ