Irmiya 25:30 - Littafi Mai Tsarki30 “Kai Irmiya kuma sai ka yi annabcin dukan waɗannan magana gāba da su, ka faɗa musu cewa, “ ‘Ubangiji zai yi ruri daga Sama, Zai yi magana daga wurin zamansa mai tsarki, Zai yi wa garkensa ruri da ƙarfi ƙwarai, Zai yi ihu kamar masu matse 'ya'yan inabi, Zai yi gāba da dukan mazaunan duniya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202030 “Yanzu ka yi annabcin dukan waɗannan maganganu a kansu ka kuma ce musu, “ ‘Ubangiji zai yi ruri daga bisa; zai yi tsawa daga mazauninsa mai tsarki ya kuma yi ruri da ƙarfi a kan ƙasarsa. Zai yi ihu kamar waɗanda suke matsin ’ya’yan inabi, yi ihu a kan dukan waɗanda suke zaune a duniya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |