Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 24:5 - Littafi Mai Tsarki

5 “Haka ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce, kamar kyawawan ɓauren nan, haka nake ganin mutanen Yahuza waɗanda aka kai su bautar talala a ƙasar Kaldiyawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kamar ’ya’yan ɓauren nan masu kyau, haka zan kula da mutanen Yahuda waɗanda aka kwaso waɗanda na fisshe su daga wannan wuri zuwa ƙasar Babiloniyawa

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 24:5
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sulusi ɗayan da ya ragu kuwa zan tura cikin wuta, Zan tace su da wuta kamar yadda akan tace azurfa, Zan gwada su kamar yadda akan gwada zinariya. Za su kira gare ni, Zan kuwa amsa musu, Zan ce, ‘Su jama'ata ne,’ Su kuma za su ce, ‘Ubangiji shi ne Allahnmu.’ ”


Ubangiji mai alheri ne, Shi mafaka ne a ranar wahala. Ya san waɗanda suke fakewa a gare shi.


Waɗanda nake ƙauna, su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka, sai ka himmantu ka tuba.


Duk da haka, ƙaƙƙarfan harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa cewa, “Ubangiji ya san nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yă yi nesa da aikata mugunta.”


Amma a yanzu da kuka san Allah, ko ma dai a ce Allah ya san ku, ta yaya za ku sāke komawa a kan raunanan al'adu marasa biyan bukata, har kuna neman komawa ga bautarsu?


In kuwa wani na ƙaunar Allah, to, Allah ya san shi.


Mun kuma sani al'amura duka suna aikatawa tare, zuwa alheri ga waɗanda suke ƙaunar Allah, wato, waɗanda suke kirayayyu bisa ga nufinsa.


Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bi na.


Sai ya amsa ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, ni ban san ku ba.’


Horon da aka yi mini ya yi kyau, Domin ya sa na koyi umarnanka.


Kafin ka hore ni nakan yi kuskure, Amma yanzu ina biyayya da maganarka.


Ya ciyar da ku da manna a jeji, abin da kakanninku ba su sani ba, domin ya koya muku tawali'u, ya jarraba ku, don ya yi muku alheri daga baya.


“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce wa dukan waɗanda aka kai bauta, wato waɗanda ya aika da su bauta daga Urushalima zuwa Babila.


Ku ji maganar Ubangiji, dukanku da aka kai ku zaman talala waɗanda na kora daga cikin Urushalima zuwa Babila.’ ”


“Saboda haka ka ce, ‘Ni Ubangiji na ce, zan tattaro ku daga cikin al'ummai, da ƙasashen da aka warwatsa ku, ni kuwa zan ba ku ƙasar Isra'ila.’


Duk da haka, sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu ba zan wulakanta su ba, ba kuwa zan ji ƙyamarsu, har da zan karya alkawarina da su ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu.


Gama na san irin shirin da na yi muku, ni Ubangiji na faɗa. Shirin alheri, ba na mugunta ba. Zan ba ku gabata da sa zuciya.


domin su kiyaye dokokina, da ka'idodina, su aikata su. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ