Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 23:30 - Littafi Mai Tsarki

30 Domin haka, ga shi, ina gāba da annabawan da suke satar maganata daga wurin junansu. Ni Ubangiji na faɗa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 “Saboda haka,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke satar maganganuna daga juna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 23:30
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma duk wani annabin da ya yi izgili yana magana da sunana, ni kuwa ban umarce shi ba, ko kuwa yana magana da sunan gumaka, wannan annabi zai mutu.’


“Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce, da yake kun yi maganar wofi, kun ga wahayin ƙarya, ina gāba da ku.


“Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce, ina gāba da kambunanku da kuke farautar rayuka da su. Zan tsintsinke su daga damatsanku, in saki rayuka waɗanda kuka farauto kamar tsuntsaye.


Amma yana ƙin masu aikata mugunta, Saboda haka har mutanensu sukan manta da su.


Zan yi gāba da su, ko da yake sun tsere wa wuta, duk da haka wuta za ta cinye su. Za ku sani ni ne Ubangiji sa'ad da na tashi yin gāba da su.


Gama Ubangiji yana lura da masu aikata adalci, Yana kuma sauraron roƙonsu. Amma Ubangiji yana gāba da masu aikata mugunta.”


Ni Ubangiji na ce, wannan zai zama muku alama, cewa zan hukunta ku a wannan wuri domin ku sani lalle maganata ta aukar muku da masifa za ta cika.


“Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan aukar muku da masifa, in hallaka mutanen Yahuza duka.


Ubangiji ba zai gafarce shi ba, amma fushin Ubangiji da kishinsa za su auko a kan wannan mutum, dukan la'anar kuma da aka rubuta a littafin nan za ta bi ta kansa, Ubangiji kuma zai shafe sunansa daga duniya.


Zan yi gāba da ku in sa maƙiyanku su ɗibge ku, waɗanda suke ƙinku za su mallake ku. Za ku yi ta gudu ba mai korarku.


Ni kaina zan yi gāba da wannan mutum, in raba shi da jama'arsa domin ya ba Molek ɗaya daga cikin 'ya'yansa, gama ya ƙazantar da alfarwa ta sujada, ya ƙasƙantar da sunana mai tsarki.


Ga shi, ina gāba da ku, ya ku mazaunan kwarin, Ya dutsen da yake a fili,’ in ji Ubangiji. ‘Ku da kuke cewa, wa zai iya gangarowa wurinku, Ko kuwa wa zai shiga wurin zamanku?


Ina kuma gāba da annabawan da suke faɗar ra'ayin kansu, sa'an nan su ce, ‘Ubangiji ne ya faɗa.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ