Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 23:28 - Littafi Mai Tsarki

28 Bari annabin da yake da mafarki ya faɗi mafarkinsa, amma wanda yake da maganata ya faɗe ta da aminci. Me ya haɗa ciyawa da alkama? Ni Ubangiji na faɗa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 Bari annabin da ya yi mafarki ya faɗa mafarkinsa, amma bari wanda yake da maganata ya yi ta da aminci. Gama me ya haɗa ciyawa da alkama?” In ji Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 23:28
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ina gode wa Almasihu Yesu Ubangijinmu, wanda ya ƙarfafa ni, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa,


Domin mu ba kamar mutane da yawa muke ba, masu yi wa Maganar Allah algus, mu kaifi ɗaya ne, kamar yadda Allah ya umarce mu, haka muke magana a gaban Allah, muna na Almasihu.


Ubangiji ya ce, “Wane ne amintaccen wakilin nan mai hikima, da ubangidansa zai ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari?


“Wane ne amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangidansa ya ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari?


Amintaccen mashaidi a ko yaushe yana faɗar gaskiya, amma marar aminci ba ya faɗar kome, sai ƙarairayi.


Har wa yau dai, abin da ake bukata ga mai riƙon amana, a same shi amintacce.


Wa yake da isasshiyar hikimar da zai fahimci wannan? Wa Ubangiji ya faɗa masa don ya sanar? Me ya sa ƙasar ta lalace ta zama kufai, har ba wanda yake iya ratsa ta, kamar hamada?


Irmiya ya ce, “Ya ku mata, ku ji maganar Ubangiji, Ku kasa kunne ga maganar da ya faɗa, Ku koya wa 'ya'yanku mata kukan makoki, Kowacce ta koya wa maƙwabciyarta waƙar makoki,


Na ji abin da annabawan nan suka ce, su da suke annabcin ƙarya da sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki!’


Annabi Irmiya kuwa ya ce musu, “Na ji abin da kuka ce. Ga shi kuwa, zan yi addu'a ga Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka roƙa. Kowace irin amsa da Ubangiji ya bayar, zan faɗa muku, ba zan ɓoye muku kome ba.”


“Ubangiji Allah ya ce kaito ga wawayen annabawa waɗanda suke bin ra'ayin zuciyarsu, ba su kuwa ga wani wahayi ba.


Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji, abin da Ubangiji ya faɗa mini, shi ne zan faɗa.”


Sarki Ahab kuwa ya ce masa, “Sau nawa zan roƙe ka kada ka faɗa mini kome sai dai gaskiya ta Ubangiji?”


Ya jama'ata, an buga ku kamar yadda ake bugun alkama a masussuka. Amma yanzu na kawo muku albishir wanda na ji daga wurin Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ