Annabin Allah kuwa ya je wurin Sarkin Isra'ila ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ‘Tun da yake Suriyawa sun ce, Ubangiji shi Allah na tuddai ne, ba Allah na kwari ba, saboda haka zan ba da dukan wannan taron jama'a a hannunka, za ka sani ni ne Ubangiji.’ ”
Fādawan Sarkin Suriya suka ce masa, “Allolinsu na tuddai ne, don haka suka fi mu ƙarfi, bari mu yi yaƙi da su a cikin kwari, ta haka za mu ci su ba shakka.