Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 23:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce a kan annabawa, “Ga shi, zan ciyar da su da abinci mai ɗaci, In shayar da su da ruwan dafi. Daga wurin annabawan Urushalima Rashin tsoron Allah ya fito ya mamaye dukan ƙasar.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da annabawa, “Zan sa su ci abinci mai ɗaci su kuma sha ruwa mai dafi, domin daga annabawan Urushalima rashin sani Allah ya bazu ko’ina a ƙasar.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 23:15
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mutanen Urushalima sun ce, “Don me muke zaune kawai? Bari mu tattaru, mu tafi cikin garuruwa masu garu, Mu mutu a can, Gama Ubangiji Allahnmu ya ƙaddara mana mutuwa, Ya ba mu ruwan dafi, Domin mun yi masa laifi.


Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan ciyar da mutanen nan da abinci mai ɗaci, in shayar da su da ruwan dafi.


Ya shayar da ni da ruwan ɗaci, Ya ƙosar da ni da abinci mai ɗaci.


Ya kewaye ni da yaƙi, Ya rufe ni da baƙin ciki mai tsanani da wahala.


Sa'ad da na ji yunwa, sai suka ba ni dafi, Sa'ad da na ji ƙishi, sai suka ba ni ruwan tsami.


Sunan tauraron kuwa Ɗaci. Sulusin ruwa ya zama mai ɗaci, sai mutane da yawa suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.


suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha, amma da ya ɗanɗana sai ya ƙi sha.


Ka tuna da azabata, da galabaitata, Da ɗacin raina, da kumallon da nake fama da shi.


Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, ta koma ga bauta wa gumakan al'umman nan. Kada a iske wani tushe a cikinku mai ba da 'ya'ya masu dafi, masu ɗaci.


Domin haka ga abin da ni Ubangiji na ce a kan annabawan da suke yin annabci da sunana, ko da yake ban aike su ba, waɗanda suke cewa, ‘Takobi da yunwa ba za su shigo ƙasan nan ba.’ Za a hallaka su da takobi da yunwa.


A wannan rana fa, ni Ubangiji Mai Runduna, zan shafe sunayen gumaka daga ƙasar, har da ba za a ƙara tunawa da su ba. Zan kuma kawar da annabawa da mugayen aljannu.


Amma suka taurare, suka biye wa zuciyarsu, suka bi Ba'al, kamar yadda kakanninsu suka koya musu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ