Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 23:13 - Littafi Mai Tsarki

13 “A cikin annabawan Samariya, Na ga abu marar kyan gani. Da sunan Ba'al suke yin annabci, Suna ɓad da jama'ata Isra'ila

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 “A cikin annabawan Samariya na ga wannan abin banƙyama. Suna annabci ta wurin Ba’al suna ɓad da mutanena Isra’ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 23:13
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Firistoci kuma ba su ce, ‘Ina Ubangiji Yake’ ba? Masanan shari'a ba su san ni ba. Masu mulki sun yi mini laifi, Annabawa sun yi annabci da sunan Ba'al, Sun bi waɗansu abubuwa marasa amfani.”


Su waɗanda suke bi da jama'an nan, sun bashe su, sun ruɗar da su ɗungum.


Ta haka kuwa Manassa ya lalatar da Yahuza da mazaunan Urushalima. Suka aikata muguntar da ta fi ta al'umman da Ubangiji ya hallaka a gaban jama'ar Isra'ila.


Iliya kuma ya ce musu, “Ku kama annabawan Ba'al, kada ku bar ko ɗaya ya tsere.” Iliya kuwa ya kai su rafin Kishon, ya karkashe su a can.


Ina kuma gāba da annabawan da suke annabcin mafarkansu na ƙarya, suna kuwa faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu, saboda rashin hankalinsu. Ni ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan jama'a ba ko kaɗan, ni Ubangiji na faɗa.”


“Ka ɗauki takarda, ka rubuta dukan maganar da na yi maka a kan Isra'ila, da Yahuza, da dukan al'ummai, tun daga ran da na fara yi maka magana a zamanin Yosiya har ya zuwa yau.


“Karuwanci, da ruwan inabi, Da ruwan inabin da bai sa hauka ba sukan kawar da hankali.


Mutanena sukan yi tambaya a wurin abin da aka yi da itace, Sandansu yakan faɗa musu gaiɓu, Gama ruhun karuwanci ya ɓad da su, Sun rabu da Allahnsu don su yi karuwanci.


Duk wannan kuwa saboda laifin Yakubu ne, Da laifin Isra'ila. Mene ne laifin Yakubu? Ashe, ba bautar gumaka da zaluncin da ake yi a Samariya ba? Mene ne kuma laifin Yahuza? Ashe, ba bautar gumaka da zaluncin da ake yi a Urushalima ba?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ