Irmiya 23:10 - Littafi Mai Tsarki10 Gama ƙasar cike take da mazinata, Saboda la'ana, ƙasar za ta yi makoki, Wuraren kiwo na jeji sun bushe, Manufarsu mugunta ce, Ba su mori ƙarfinsu a inda ya kamata ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Ƙasar ta cika da mazinata; saboda la’ana ƙasar ta zama kango makiyaya a hamada ta bushe. Annabawa suna bin mugayen muradu suna kuma amfani da ƙarfinsu a hanyar marar kyau. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”