Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 22:8 - Littafi Mai Tsarki

8 “Al'ummai masu yawa za su wuce ta gefen wannan birni, kowane mutum zai ce wa maƙwabcinsa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 “Mutane daga al’ummai da yawa za su ratsa cikin wannan birni su kuma tambayi juna suna cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 22:8
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya Ubangiji, kai mai adalci ne, amma mu sai kunya, kamar yadda yake a yau ga mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima da dukan Isra'ilawa, waɗanda suke kusa da waɗanda suke nesa a dukan ƙasashen da ka kora su saboda rashin amincin da suka yi maka.


Sarakunan duniya da mazaunanta ba su gaskata, Cewa abokan gaba ko maƙiya Za su iya shiga ƙofofin Urushalima ba.


“Sa'ad da ka faɗa wa mutanen nan wannan magana duka, za su kuwa ce maka, ‘Me ya sa Ubangiji ya hurta wannan babbar masifa a kanmu? Mene ne laifinmu? Wane irin zunubi muka yi wa Ubangiji Allahnmu?’


Shugaban matsara ya ware Irmiya, sa'an nan ya ce masa, “Ubangiji Allahnka ne ya hurta wannan masifa a kan wurin nan.


“‘Za ki zama abin zargi, da abin ba'a, da abin faɗaka, da abin tsoro ga al'ummai da suke kewaye da ke sa'ad da na hukunta ki da zarin fushina, ni Ubangiji na faɗa.


Amma zan bar kaɗan daga cikinsu su tsere wa takobi, da yunwa, da annoba, don su tuba, su hurta dukan ayyukansu na banƙyama a cikin al'ummai inda suka tafi. Za su sani ni ne Ubangiji.”


Bisa ga halinsu da ayyukansu za ka gane abin da na yi musu ba kawai ba ne,’ ni Ubangiji na faɗa.”


Al'ummai kuma za su sani an kai jama'ar Isra'ila zaman bautar talala saboda muguntarsu, domin sun yi mini ha'inci, ni kuwa na kawar da fuskata daga gare su, na bashe su a hannun abokan gābansu, suka ci su da yaƙi.


Ga shi kuwa, ya yi kamar yadda ya faɗa, domin kun yi wa Ubangiji zunubi, ba ku yi biyayya da muryarsa ba, don haka wannan masifa ta auko muku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ