Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 22:30 - Littafi Mai Tsarki

30 Haka Ubangiji ya ce, “Rubuta wannan mutum, marar 'ya'ya. Mutumin da ba zai yi albarka a duk kwanakinsa ba. Gama ba wani daga zuriyarsa Da zai gāji gadon sarautar Dawuda, Ko ya yi mulki kuma a Yahuza.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka rabu da wannan mutum sai ka ce marar ’ya’ya, mutumin da ba zai yi nasara a rayuwarsa ba, gama babu zuriyarsa da za tă yi nasara babu wani da zai zauna a kursiyin Dawuda ko ya ƙara yin mulkin Yahuda.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 22:30
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka Ubangiji ya ce Yehoyakim, Sarkin Yahuza, ba zai sami magāji wanda zai zauna a gadon sarautar Dawuda ba. Za a jefar da gawarsa a waje ta sha zafin rana, da dare kuma za ta sha matsanancin sanyi.


Ba ruwanka da alƙalai azzalumai, marasa gaskiya, Waɗanda suka mai da rashin gaskiya ita ce gaskiyarsu,


Makiyayan dakikai ne, Ba su roƙi Ubangiji ba, Don haka ba su sami wadata ba, An watsa dukan garkensu.


Da hannuwanku a kā za ku komo daga Masar don kunya. Gama waɗanda kuke dogara gare su, ni Ubangiji, na ƙi su, Ba za ku yi arziki tare da su ba.”


ka ce, ‘Ka ji maganar Ubangiji, ya Sarkin Yahuza, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda kai da barorinka, da mutanenka waɗanda suke shiga ta ƙofofin nan.


saboda haka Ubangiji ya ce, ‘ga shi, zan hukunta Shemaiya, mutumin Nehelam, shi da zuriyarsa ba za a bar masa mai rai ko ɗaya a wannan jama'a ba, wanda zai ga irin alherin da zan yi wa jama'ata, gama ya kuta tayarwa ga Ubangiji,’ ” in ji Ubangiji.


Ya kuwa kashe 'ya'yan Zadakiya a idonsa. Ya kuma kashe dukan shugabannin Yahuza a Ribla.


Ba shi da zuriya, da sauran waɗanda suka ragu da rai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ