Dukanku ku ji, ku al'ummai! Ki kasa kunne, ya duniya, da dukan abin da yake cikinki. Bari Ubangiji Allah Daga Haikalinsa mai tsarki ya zama shaida a kanku.
to, yau na kira sama da duniya su shaida a kanku, cewa lalle za ku hallaka nan da nan cikin ƙasar da za ku haye Urdun zuwa cikinta don ku mallake ta. Ba za ku daɗe cikinta ba, amma za a shafe ku ƙaƙaf.