Irmiya 22:28 - Littafi Mai Tsarki28 Ashe, Yekoniya kamar fasasshen tulu yake, Wanda ba wanda ya kula da shi? Me ya sa aka watsar da shi da 'ya'yansa, A ƙasar da ba su sani ba? အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202028 Wannan mutum Yehohiyacin ne da aka rena, fasasshen tukunya, abin da babu wanda yake so? Me ya sa za a jefar da shi da ’ya’yansa a jefar da su a ƙasar da ba su sani ba? အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kama Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, daga Urushalima, ya kai shi bautar talala a Babila, tare da sarakunan Yahuza, da gwanayen sana'a, da maƙera, dukansu, ya kawo su Babila. Sai Ubangiji ya nuna mini wannan wahayi. Na ga kwando biyu na ɓaure, an ajiye su a gaban Haikalin Ubangiji.