Ba waɗansu daga cikin mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, da za su tsere ko su rayu. Ba wani daga cikinsu da zai koma Yahuza inda suke marmarin komawa da zama, ba wanda zai koma, sai dai 'yan gudun hijira.”
Gama haka Ubangiji ya ce a kan Yahowahaz, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, wanda ya gāji sarautar ubansa, Yosiya, wanda ya tafi ya bar wurin nan. Ba zai ƙara komowa nan ba.
Zan kuma komo da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, da dukan waɗanda aka kai su zaman talala daga Yahuza, gama zan karya karkiyar Sarkin Babila.’ ”
“Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa'ad da kuka tafi Masar. Za ku zama najasa, da abin ƙyama, da la'ana, da abin ba'a. Wannan wuri kuwa ba za ku ƙara ganinsa ba.’
Ku mutanen Yahuza, kada ku yi kuka saboda sarki Yosiya, Kada ku yi makokin rasuwarsa, Amma ku yi kuka ƙwarai saboda ɗansa Yehowahaz. Sun ɗauke shi, sun tafi da shi, ba zai ƙara komowa ba, Ba kuma zai ƙara ganin ƙasar da aka haife shi ba.