Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 22:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Ya ku mazaunan Lebanon, Waɗanda suke zaune cikin itatuwan al'ul, Irin nishin da za ku yi sa'ad da azaba ta same ku, Azaba ce irin ta mace mai naƙuda!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Kai da kake zama a ‘Lebanon,’ kai da kake sheƙa a gine-ginen al’ul za ka yi nishi sa’ad da zafi ya auka maka, zafi kamar na mace mai naƙuda!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 22:23
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mutanen Urushalima sun ce, “Mun ji labarin yaƙin, Hannuwanmu suka yi rauni. Azaba ta kama mu, Ciwo irin na mai naƙuda.


Abin da Ubangiji ya ce ke nan a kan fādar Sarkin Yahuza, “Kyanta kamar Gileyad take a gare ni, Kamar kuma ƙwanƙolin Lebanon. Duk da haka zan maishe ta hamada, Birnin da ba kowa ciki.


“Tasa ta ƙare, shi wanda ya arzuta gidansa da ƙazamar riba, Ya kuma gina gidansa a bisa don ya tsere wa masifa!


Ko da yake kina shawagi can sama kamar gaggafa, Gidanki kuma yana can cikin taurari, Daga can zan saukar da ke,” in ji Ubangiji.


Ko da za su nutsa zuwa lahira, Zan kama su. Ko sun hau Sama, Zan turo su.


Ba su yi kuka gare ni da zuciya ɗaya ba, Sa'ad da suke kuka a gadajensu, Sun tsattsaga jikinsu domin abinci da ruwan inabi. Sun yi mini tawaye.


“Zan koma wurin zamana Sai lokacin da suka yarda sun yi zunubi, su neme ni. A cikin ƙuncinsu za su neme ni.”


Tsoronki da ake ji da girmankanki sun ruɗe ki, Ke da kike zaune a kogon dutse, a kan tsauni, Ko da yake kin yi gidanki can sama kamar gaggafa, Duk da haka zan komar da ke ƙasa, Ni Ubangiji na faɗa.”


“Ku mazaunan Mowab, ku bar garuruwanku, Ku tafi, ku zauna a kogwanni, Ku zama kamar kurciya wadda take yin sheƙarta a bakin kwazazzabo.


Ga shi, ina gāba da ku, ya ku mazaunan kwarin, Ya dutsen da yake a fili,’ in ji Ubangiji. ‘Ku da kuke cewa, wa zai iya gangarowa wurinku, Ko kuwa wa zai shiga wurin zamanku?


An ji murya a kan filayen tuddai, Kūka da roƙo ne na 'ya'yan Isra'ila maza, Domin sun rabu da hanyarsu, Sun manta da Ubangiji Allahnsu.


Sai kuma ya dubi Keniyawa, ya hurta jawabinsa, ya ce, “Wurin zamanku mai ƙarƙo ne, Gidajenku kuma suna cikin duwatsu.


Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai, da dogayen gasusuwan fikafikai da gasusuwa da yawa masu launi iri iri, ta zo Lebanon ta ciri kan itacen al'ul.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ