Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 22:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Ku mutanen Yahuza, kada ku yi kuka saboda sarki Yosiya, Kada ku yi makokin rasuwarsa, Amma ku yi kuka ƙwarai saboda ɗansa Yehowahaz. Sun ɗauke shi, sun tafi da shi, ba zai ƙara komowa ba, Ba kuma zai ƙara ganin ƙasar da aka haife shi ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Kada ku yi kuka domin sarkin da ya mutu ko ku yi makoki saboda rashinsa; a maimako, ku yi kuka mai zafi saboda wanda aka kai zaman bauta, domin ba zai ƙara dawowa ba ko ya ƙara ganin ƙasarsa ta haihuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 22:10
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama haka Ubangiji ya ce a kan Yahowahaz, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, wanda ya gāji sarautar ubansa, Yosiya, wanda ya tafi ya bar wurin nan. Ba zai ƙara komowa nan ba.


Ina ƙyashin waɗanda suka mutu, gama sun fi waɗanda suke da rai yanzu jin daɗi.


Gara ma waɗanda takobi ya kashe Da waɗanda yunwa ta kashe, Gama sun rame sarai saboda rashin abinci.


Adalin mutum yakan mutu, amma ba wanda ya kula. An kwashe mutanen kirki ba kuwa wanda ya kula, an tsame adali daga cikin bala'i.


Domin haka, ba za ka ga hukuncin da yake zuwa a kan Urushalima ba, za a kai ka cikin kabarinka lafiya.’ ” Mutanen kuwa suka mayar wa sarki Yosiya da wannan magana.


Amma Yesu ya juya gare su, ya ce, “Ya ku matan Urushalima, ku bar yi mini kuka, sai dai ku yi wa kanku da kuma 'ya'yanku,


Domin haka ga abin da Ubangiji ya ce a kan Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, “Ba za su yi makoki dominsa ba, ko su ce, ‘Wayyo ɗan'uwanmu!’ ko, ‘Wayyo 'yar'uwarmu!’ Ba za su yi makoki dominsa ba, su ce, ‘Wayyo ubangidanmu!’ ko ‘Wayyo mai martaba!’


Sarkin Masar ya naɗa Eliyakim, ɗan'uwansa, sarki a Yahuza da Urushalima. Ya sa masa sabon suna Yehoyakim. Amma Neko ya ɗauko Yehowahaz ɗan'uwan Eliyakim ya kai shi Masar.


Ba wanda zai ba mai makoki abinci don ya ta'azantar da shi saboda mamacin, ba kuma wanda zai ba shi abin sha don ya ta'azantar da shi saboda mahaifinsa ko mahaifiyarsa.


“Za ka kuma faɗa musu cewa, ‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ku sha, ku bugu, ku yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku tashi saboda takobin da zan aiko muku.’


Zan kuma komo da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, da dukan waɗanda aka kai su zaman talala daga Yahuza, gama zan karya karkiyar Sarkin Babila.’ ”


“Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa'ad da kuka tafi Masar. Za ku zama najasa, da abin ƙyama, da la'ana, da abin ba'a. Wannan wuri kuwa ba za ku ƙara ganinsa ba.’


Ba waɗansu daga cikin mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, da za su tsere ko su rayu. Ba wani daga cikinsu da zai koma Yahuza inda suke marmarin komawa da zama, ba wanda zai koma, sai dai 'yan gudun hijira.”


“Ya ɗan mutum, ga shi, ina gab da ɗauke maka ƙaunatacciyarka farat ɗaya, amma fa, kada ka yi makoki, ko kuka, ko ka zubar da hawaye.


A zamaninsa Fir'auna-neko, Sarkin Masar, ya tafi ya tasar wa Sarkin Assuriya da yaƙi a Kogin Yufiretis. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa'ad da Fir'auna-neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Magiddo.


Amma ƙasan nan da suke marmarin komowa cikinta, ba za su koma cikinta ba.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ