Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 21:4 - Littafi Mai Tsarki

4 “Ku faɗa wa Zadakiya, Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ga shi, zan juyo kayan yaƙin da suke hannunka waɗanda kake yaƙi da su gāba da Sarkin Babila, da sojojinsa, waɗanda suka kewaye garun birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yake cewa ina shirin juya kayan yaƙin da suke a hannuwanka a kanka, waɗanda kake amfani don ka yaƙi sarki Babilon da kuma Babiloniyawa waɗanda suka kewaye katangar birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 21:4
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Sa'ad da ake zuwa yaƙi da Kaldiyawa gidaje za su cika da gawawwakin mutane waɗanda na kashe da fushina da hasalata, gama na ɓoye wa wannan birni zatina saboda dukan muguntarsu.


Sarkin Babila kuwa zai tafi da Zadakiya zuwa Babila. Zai zauna can sai lokacin da na ziyarce shi. Ko da ya yi yaƙi da Kaldiyawa ba zai yi nasara ba.”


Ji hayaniyar da ake yi a duwatsu da amon babban taron jama'a. Amon al'ummai da mulkoki suna tattaruwa. Ubangiji Mai Runduna yana shirya mayaƙansa domin yaƙi.


“Ga abin da zan yi wa gonar inabina. Zan cire shingen da yake kewaye da ita, in rushe bangon da ya kāre ta, in bar namomin jeji su cinye ta, su tattake ta.


Gama zan tattara dukan al'ummai su yi yaƙi da Urushalima. Za a ci birnin, a washe gidajen. Za a yi wa mata faɗe. Za a kai rabin mutanen birnin bauta, amma za a bar sauran mutanen a cikin birnin.


Ubangiji ya wulakanta bagadensa, Ya kuma wofinta tsattsarkan Haikalinsa. Ya ba da garun fādodinta a hannun abokan gāba, Suka yi sowa a Haikalin Ubangiji Kamar a ranar idi.


Ubangiji ya zama kamar maƙiyi, ya hallaka Isra'ila. Ya hallaka fādodinta duka, Ya mai da kagaranta kango. Ya aukar wa Yahuza da makoki da baƙin ciki mai yawa.


Sa'an nan da aka ci Urushalima, sai dukan sarakunan Sarkin Babila suka shiga, suka zauna a Ƙofar Tsakiya. Sarakuna, su ne Nergal-sharezer, da Samgar-nebo, da Sarsekim, wato Rabsaris, da Nergal-sharezer, wato Rabmag, da dukan sauran shugabannin Sarkin Babila.


Sarki ya yi fushi, ya tura sojansa, suka hallaka masu kisankan nan, suka ƙone garinsu ƙurmus.


Ko sun goyi 'ya'ya, Zan sa su mutu tun ba su balaga ba. Tasu ta ƙare sa'ad da na rabu da su!”


Suka kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da daruna, da tasoshin ƙona turare, da kayayyakin tagulla waɗanda ake amfani da su domin hidimar Haikali.


Za a kashe ku a yaƙi, ko a kwashe ku, kamammun yaƙi. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.


Haka Ubangiji ya ce, ‘Ga shi, zan maishe ka abin tsoro ga kai kanka, da dukan abokanka. Abokan gābansu za su kashe su da takobi a kan idonka. Zan ba da dukan Yahuza a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai kwashe waɗansu ya kai bautar talala a Babila, ya kuma kashe waɗansu da takobi.


Zadakiya Sarkin Yahuza, ya sa shi a kurkuku, gama ya ce, “Don me kake yin annabci? Ka ce, Ubangiji ya ce, ga shi, zai ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa cinye shi da yaƙi.


“Ga shi, Kaldiyawa sun gina mahaurai kewaye da birnin da suka kewaye shi da yaƙi. Saboda takobi, da yunwa, da annoba aka ba da birnin a hannun Kaldiyawa, waɗanda suke yaƙi da birnin. Abin da ka faɗa ya tabbata, ka kuwa gani.


Domin haka, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na ce zan kawo wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima masifar da na ce zan kawo musu, domin na yi musu magana, ba su ji ba, na kira su, ba su amsa ba.”


Da zafin fushinsa, ya karya ƙarfin Isra'ila, Ya kuma bar yi musu taimako A lokacin da abokan gāba suka zo. Kamar harshen wuta, ya ƙone dukan abin da yake na Yakubu.


Sa'an nan zan karya bakan da yake a hannun hagunka, in sa kiban da suke a hannun damanka su fāɗi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ