Irmiya 21:2 - Littafi Mai Tsarki2 “Ka tambayar mana Ubangiji, gama Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kawo mana yaƙi. Ko Ubangiji zai yi mana al'amuran nan nasa masu ban al'ajabi kamar yadda ya saba, ya sa Sarkin Babila ya janye, ya rabu da mu?” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 “Yanzu ka roƙi mana Ubangiji saboda Nebukadnezzar sarkin Babilon yana kawo mana yaƙi. Wataƙila Ubangiji zai yi mana waɗansu abubuwa banmamaki kamar a lokacin baya don yă janye daga gare mu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji kuwa ya aiki mala'ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.
Suka sāke yin tambaya ga Ubangiji suka ce, “Mu sāke tafiya mu yi yaƙi da 'yan'uwanmu, mutanen Biliyaminu, ko kuwa mu bari?” Ubangiji kuwa ya ce musu, “Ku je, gama gobe zan ba da su gare ku.” A lokacin nan akwatin alkawari na Ubangiji yana nan. Finehas ɗan Ele'azara, ɗan Haruna, shi ne mai aiki a gabansa.