Irmiya 20:9 - Littafi Mai Tsarki9 Idan na ce, ‘Ba zan ambaci Ubangiji ba, Ban zan ƙara yin magana da sunansa ba,’ Sai in ji damuwa a zuciyata, An kulle ta a ƙasusuwana, Na gaji da danne ta a cikina, Ba zan iya jurewa ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Amma in na ce, “Ba zan ambace shi ba ba zan ƙara yin magana da sunansa ba,” sai in ji maganarsa a cikina kamar wuta, wutar da aka kulle a ƙasusuwana. Na gaji da danne ta a cikina; tabbatacce ba zan iya ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Don haka ina cike da fushin Ubangiji Na gaji da kannewa. Ubangiji ya ce, “Zan kwararo fushi kan yara da suke a titi. Da kuma kan tattaruwar samari. Za a ɗauke mata da miji duka biyu, Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufa tukub-tukub. Za a ba waɗansu gidajensu, da gonakinsu, da matansu, Gama zan nuna ikona in hukunta mazaunan ƙasar.