Irmiya 20:16 - Littafi Mai Tsarki16 Bari wannan mutum ya zama kamar biranen da Ubangiji ya kaɓantar ba tausayi. Bari ya ji kuka da safe, Da rana kuma ya ji gangamin yaƙi, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202016 Bari mutumin ya zama kamar garuruwan da Ubangiji ya tumɓuke ba tausayi. Bari yă ji kuka da safe kururuwan yaƙi kuma da tsakar rana. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ina roƙonka, ya Ubangiji, ashe, dā ma can ban faɗa ba, kafin in bar gida, cewa irin abin da za ka yi ke nan? Ai, dalilin da ya sa na yi iyakar ƙoƙarina in gudu zuwa Tarshish ke nan. Na sani kai mai taushin hali ne, mai jinƙai, mai haƙuri. Kai kullum mai alheri ne, a shirye kake kuma ka dakatar da nufinka na yin hukunci.