Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 20:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Amma Ubangiji kana tare da ni Kamar jarumi mai bantsoro, Don haka masu tsananta mini za su yi tuntuɓe, Ba za su rinjaye ni ba. Za su sha kunya ƙwarai, Gama ba za su yi nasara ba. Ba za a manta da su ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Amma Ubangiji yana tare da ni kamar babban jarumi; saboda haka masu tsananta mini za su yi tuntuɓe ba kuwa za su yi nasara ba. Za su fāɗi su kuma sha mummunar kunya; ba za a taɓa manta da rashin bangirmansu ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 20:11
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za su yi gāba da kai, amma ba za su ci nasara a kanka ba, gama ina tare da kai, ni Ubangiji na faɗa.”


Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai, Zan kiyaye ka. Ni Ubangiji na faɗa.”


Zan maishe ka garun tagulla saboda waɗannan mutane, Za su yi yaƙi da kai, amma ba za su yi nasara a kanka ba, Gama ina tare da kai don in cece ka, in kuɓutar da kai.


Bari waɗanda suka tsananta mini su sha kunya, Amma kada ka bar ni in kunyata. Bari su tsorata, Amma kada ka bar ni in tsorata. Ka aukar musu da ranar masifa, Ka hallaka su riɓi biyu!


Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.


Abokan gābana duka za su sha kunyar fāɗuwarsu, Suna cikin matsanancin ruɗami, Za a kwashe su farat ɗaya.


Ka sa masu so su kashe ni, A ci nasara a kansu, su ruɗe! Ka sa waɗanda suke murna saboda wahalaina Su koma baya, su sha kunya!


Ka sa waɗanda suka ƙyaface ni a wahalata, A rinjaye su, su ruɗe. Ka sa waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni, Su sha kunya da wulakanci!


To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?


Zan sa ku zama abin zargi da abin kunya har abada, ba kuwa za a manta da wannan ba.”


Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya ba ni ƙarfin sanar da bishara sosai da sosai, domin duk al'ummai su ji, aka kuwa cece ni daga bakin zaki.


Su waɗanda suka yi gumaka, dukansu za su sha kunya, Dukansu za su zama abin kunya.


Zo, ka ga abin da Allah ya yi, Ayyukansa masu ban al'ajabi Waɗanda ya aikata ga mutane.


Waɗanda suka rasu za su tashi, waɗansu zuwa rai madawwami, waɗansu kuwa zuwa kunya da madawwamin ƙasƙanci.


Ka amsa mana, ya Allah Mai Cetonmu, Ka kuma cece mu ta wurin aikata al'amuran banmamaki. Mutane daga ko'ina a duniya, Har da waɗanda suke can nesa a hayin tekuna, Sun dogara gare ka.


A ji tsoron Ubangiji Mai Iko Dukka, Shi babban Sarki ne, ya mallaki dukan duniya.


Ubangiji ya ce, “Isra'ila, ku kima ne marasa ƙarfi kuma, Kada ku ji tsoro, zan taimake ku. Ni Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ni ne mai fansarku.


“Maƙiyana suka tsananta mini da mugunta, Tun ina ƙarami, Amma ba su yi nasara da ni ba.


Sa'an nan Irmiya ya ce, “Ya Ubangiji, ka sani. Kai ne, ka ziyarce ni, Ka kuma sāka wa waɗanda suke tsananta mini. Ka sani saboda kai nake shan zargi.


Iska za ta kwashe shugabanninku, Za a kai ƙaunatattunku cikin bauta, Sa'an nan za ku sha kunya ku ruɗe, Saboda dukan muguntarku.


Kakan nuna madawwamiyar ƙauna ga dubbai, amma kakan hukunta wa 'ya'ya saboda laifin ubanninsu. Ya maigirma Maɗaukaki, Allah, sunanka kuwa Ubangiji Mai Runduna.


Ni kuwa, ga shi, yau na maishe ka birni mai kagara, da ginshiƙin ƙarfe, da bangon tagulla ga dukan ƙasar, da sarakunan Yahuza, da shugabanninta, da firistocinta, da mutanen ƙasar.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ