Ya ku mutanen Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji, Gama Ubangiji yana da shari'a da ku, ku mazaunan ƙasar. “Gama ba gaskiya, ko ƙauna, Ko sanin Ubangiji a ƙasar.
Za ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ya ku sarakunan Yahuza da mazaunan Urushalima, Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, zan kawo wata irin masifa a wannan wuri, wanda duk ya ji, kunnuwansa za su kaɗa.
“Ka tafi ka tsaya a ƙofar Haikalin Ubangiji, ka yi shelar wannan magana, ka ce, su kasa kunne ga maganar Ubangiji, dukansu mutanen Yahuza, su da suke shiga ta ƙofofin nan don su yi wa Ubangiji sujada!
Isra'ila tsattsarka ce ta Ubangiji, Nunar fari ta girbina. Dukan waɗanda suka ci daga cikinki sun yi laifi, Masifa za ta auko miki. Ni Ubangiji, na faɗa.”