Irmiya 2:20 - Littafi Mai Tsarki20 “Ya Isra'ila, tun da daɗewa, ka ƙi yarda Ubangiji ya mallake ka, Ka ƙi yin biyayya da ni, Ka kuwa ce, ‘Ba zan yi bauta ba.’ Amma ka yi karuwanci a kan kowane tudu, Da kowane ɗanyen itace. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202020 “Tun da daɗewa ka karya karkiyarka ka kuma tsintsinke sarƙoƙinka; sai ka ce, ‘Ba zan bauta maka ba!’ Tabbatacce, a kan kowane tudu mai tsayi da kuma a ƙarƙashin kowane ɗanyen itace ka kwanta kamar karuwa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |