“Ku yi shelarsa cikin garuruwan Masar, Cikin Migdol, da Memfis, da Tafanes, Ku ce, ‘Ku tsaya, ku yi shiri, Gama takobi yana cin waɗanda suke kewaye da ku!’
Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan dukan Yahudawan da suke zaune a ƙasar Masar, a garin Migdol, da Tafanes, da Memfis, da dukan ƙasar Fatros, ya ce,
Zan kunna wa Masar wuta. Felusiyum za ta sha azaba mai tsanani, No kuwa za a tayar mata da hankali, Za a rurrushe garukanta. Za a tasar wa Memfis dukan yini.
Ubangiji Allah ya ce, “Zan hallakar da gumaka Da siffofi a Memfis. Ba za a ƙara samun hakimi a ƙasar Masar ba, Saboda haka zan aukar da tsoro a ƙasar Masar.
Za su sheƙa cikin ƙasar Yahuza kamar rigyawa wadda ta kai har kafaɗa, ta rufe kome da kome.” Allah yana tare da mu! Fikafikansa a buɗe suke su tsare ƙasar.
Fir'auna-neko ya sa shi a kurkuku a Ribla a ƙasar Hamat, don kada ya yi mulki a Urushalima. Ya kuma sa ƙasar ta riƙa ba da gandu, wato haraji, talanti ɗari na azurfa da talanti guda na zinariya.
Ga shi yanzu, kana dogara ga Masar, wannan karyayyen sandan kyauro, wanda yakan yi wa hannun mutumin da yake tokarawa da shi sartse. Haka Fir'auna Sarkin Masar, yake ga dukan waɗanda suke dogara gare shi.’
“A ƙarƙashin inuwar Heshbon 'yan gudun hijira suna tsaye ba ƙarfi. Gama wuta ta ɓullo daga Heshbon, Harshen wuta kuma ya fito daga Sihon, Ta ƙone goshin Mowab da ƙoƙwan kai na 'yan tayarwa.
Ga shi kuma, suna tafiya zuwa halaka, Masar za ta tattara su, Memfis za ta binne su. Ƙayayuwa za su mallaki abubuwan tamaninsu na azurfa. Sarƙaƙƙiya za ta tsiro a cikin alfarwansu.