Ubangiji ya ce, “Kuna tsammani na kori mutanena Kamar yadda mutum yakan saki mata tasa? To, in haka ne ina takardar kisan auren? Kuna tsammani na sayar da ku cikin bauta Kamar mutumin da ya sayar da 'ya'yansa? A'a, kun tafi bauta ne saboda da zunubanku, Aka tafi da ku saboda da laifofinku.
Na sayo bayi mata da maza, an kuma haifa mini cucanawa a gidana. Ina kuma da manyan garkunan shanu, da na tumaki, da na awaki fiye da dukan wanda ya taɓa zama a Urushalima.
“Sa'ad da mutanenki suka ce, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi mana waɗannan abubuwa duka?’ Sai ki ce musu, ‘Kamar yadda kuka rabu da ni kuka bauta wa gumaka a ƙasarku, haka kuma za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’ ”
Za ku rasa abin da yake hannunku daga cikin gādon da na ba ku. Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama da fushina wuta ta kama wadda za ta yi ta ci har abada.”