Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 2:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Akwai wata al'umma da ta taɓa sāke gumakanta Ko da yake su ba kome ba ne? Amma mutanena sun sauya darajarsu da abin da ba shi da rai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Akwai wata al’ummar da ta canja allolinta? (Duk da haka su ba alloli ba ne sam.) Amma mutanena sun musayar da ɗaukakarsu da gumakan banza.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 2:11
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sun sauya ɗaukakar Allah marar mutuwa da misalin siffar mutum mai mutuwa, da ta tsuntsaye, da ta dabbobi, da kuma ta masu jan ciki.


suka ƙaƙƙone gumakansu waɗanda ba Allah ba ne ko kaɗan, siffofi ne kurum na itace da na dutse, da mutane suka yi da hannuwansu.


Mutum zai iya yi wa kansa alloli? Ai, waɗannan ba alloli ba ne!”


Suka musaya ɗaukakar Allah Da siffar dabba mai cin ciyawa.


Ko da yake al'ummai suna bin gumakansu, Amma mu za mu bi Ubangiji Allahnmu har abada abadin.


A game da cin abin da aka yanka wa gumaka kuwa, mun sani, duk duniyar nan gunki yana a matsayin abin da babu ne, da kuma, babu wani Allah sai ɗaya.


Firistoci kuma ba su ce, ‘Ina Ubangiji Yake’ ba? Masanan shari'a ba su san ni ba. Masu mulki sun yi mini laifi, Annabawa sun yi annabci da sunan Ba'al, Sun bi waɗansu abubuwa marasa amfani.”


Ubangiji ya ce, “Wane laifi ne na yi wa kakanninku, Da suka bar bina? Suka bauta wa gumaka marasa amfani, Su kuma suka zama marasa amfani.


Amma nasu alloli na azurfa da zinariya ne, Da hannu aka siffata su.


Amma kai, ya Ubangiji, kullum kana kiyaye ni daga hatsari, Kana ba ni nasara, Kana kuma maido mini da ƙarfin halina.


Mai farin ciki ne kai, ya Isra'ila! Wane ne kamarku, mutanen da Ubangiji ya ceta? Ubangiji ne garkuwarku, Shi ne kuma takobinku mai daraja. Magabtanku za su yi muku fādanci, Amma ku za ku tattake masujadansu.”


Domin kun sani an fanshe ku ne daga al'adunku na banza da wofi da kuka gāda, ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa da zinariya ba,


Dā da ba ku san Allah ba, kuna bauta wa waɗansu gumaka, waɗanda ga ainihi ba a bakin kome suke ba.


Sai ta sa wa yaron suna Ikabod, wato ɗaukaka ta rabu da Isra'ila domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma surukinta da mijinta sun rasu.


Ashe, ba ku kori firistocin Ubangiji, 'ya'yan Haruna, maza, da Lawiyawa ba, kuka yi wa kanku firistoci kamar na al'umman sauran ƙasashe? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don ya tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba.


“Don me zan gafarce ki? 'Ya'yanki sun rabu da ni, Sun yi rantsuwa da gumaka, Na ciyar da su har sun ƙoshi sosai, Suka yi karuwanci, suka ɗunguma zuwa gidajen karuwai,


“Domin haka ni Ubangiji na ce, ‘Ka tambayi sauran al'umma. Wa ya taɓa jin irin wannan? Budurwa Isra'ila, ta yi mugun abu ƙwarai!


Domin haka ni na ce, ‘Da yake kin cika rikici fiye da sauran ƙasashen da suke kewaye da suke, kin ƙi yin tafiya cikin dokokina, ba ki kiyaye ka'idodin ba, amma kin bi ka'ikodin al'umman da take kewaye da ke,


domin in kama zukatan mutanen Isra'ila waɗanda suka zama baƙi a gare ni, saboda gumakansu.


Suka sa shi kishi, saboda gumaka, Suka tsokani fushinsa da abubuwan banƙyama.


Suka sa ni kishi da abin da ba Allah ba, Suka tsokani fushina da gumakansu, Ni kuma zan sa su su yi kishi da waɗanda suke ba mutane ba. Zan tsokane su da wawanyar al'umma.


Domin Sulemanu ya rabu da ni, ya bauta wa Ashtoret, gunkiyar Sidoniyawa, da Kemosh, gunkin Mowab, da Milkom, gunkin Ammonawa. Bai yi tafiya a cikin tafarkuna ba, bai yi abin da yake daidai a gare ni ba, bai kiyaye dokokina, da ka'idodina kamar yadda Dawuda, tsohonsa, ya yi ba.


Sai mala'ikan Ubangiji ya yi magana da Iliya Batishbe, ya ce, “Tashi, ka tafi, ka sadu da manzannin Sarkin Samariya, ka ce musu, ‘Ba Allah a Isra'ila da za ku tafi ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron?’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ