Bari annabin da yake da mafarki ya faɗi mafarkinsa, amma wanda yake da maganata ya faɗe ta da aminci. Me ya haɗa ciyawa da alkama? Ni Ubangiji na faɗa.
in tafi in yi shelar abin da Ubangiji ya ce a kunnen Urushalima, in ce, “Na tuna da amincinki a lokacin ƙuruciyarki, Da ƙaunarki kamar ta amarya da ango. Yadda kika bi ni a cikin jeji, da a ƙasar da ba a shuka ba.
Can zan ba ta gonar inabi, In mai da kwarin Akor, wato wahala, ƙofar bege. A can za ta amsa mini kamar a kwanakin ƙuruciyarta, Kamar lokacin da ta fito daga ƙasar Masar.