Ubangiji ya ce mini, “Tafi ka sayo tulu a wurin maginin tukwane. Sa'an nan kuma ka ɗauki waɗansu daga cikin dattawan jama'a, da waɗansu manyan firistoci,
Za a ragargaza ku kamar tukunyar yumɓu, da mummunar ragargazawa har da ba za a sami 'yar katangar da za a ɗauki garwashin wuta ba, ko a ɗebo ruwa daga randa.”