Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 18:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Bari a ji kururuwa daga gidajensu, Saboda maharan da ka aika musu farat ɗaya, Gama sun haƙa rami don in fāɗa, Sun kafa wa ƙafafuna tarkuna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Bari a ji kuka daga gidajensu sa’ad da ka kawo masu hari a kansu farat ɗaya, gama sun haƙa rami don su kama ni suka kuma kafa tarko wa ƙafafuna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 18:22
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ya mutanena, ku sa tufafin makoki, Ku yi birgima cikin toka, Ku yi makoki mai zafi irin wanda akan yi wa ɗa tilo, Gama mai hallakarwa zai auko mana nan da nan.”


Masu girmankai sun kafa mini tarko, Sun shimfiɗa ragar igiya, Sun kuma kakkafa tarkuna a hanya don su kama ni.


Ranar busar ƙaho da yin kururuwar yaƙi Gāba da birane masu garu da hasumiyai masu tsawo.


Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su burma shi cikin maganarsa.


Na ji mutane da yawa suna sa mini laƙabi cewa, ‘Razana ta kowace fuska,’ Suna cewa, ‘Mu la'anta shi! Mu la'anta shi!’ Har ma da abokaina shaƙiƙai Suna jira su ga fāɗuwata. Suka ce, ‘Watakila a ruɗe shi, Sa'an nan ma iya rinjayarsa Mu ɗauki fansa a kansa.’


Daidai ne a rama alheri da mugunta? Duk da haka sun kafa wa raina tarko. Ka tuna yadda na tsaya a gabanka, Na yi maganar alheri a kansu, Domin ka janye fushinka daga gare su.


Na ji kuka kamar na mace wadda take naƙuda, Na ji nishi kamar na mace a lokacin haihuwarta ta fari, Na ji kukan 'yar Sihiyona tana kyakyari, Tana miƙa hannuwanta tana cewa, “Wayyo ni kaina, gama ina suma a gaban masu kisankai!”


Ku yi ihu, ku mutanen Gallim! Ku kasa kunne, ku mutanen Layish! Ku amsa, ku mutanen Anatot!


Masu son kashe ni, sun haƙa mini tarkuna, Masu so su cuce ni, suna barazanar lalatar da ni, Yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.


Masu girmankai, waɗanda ba su biyayya da dokarka, Sun haƙa wushefe don su kama ni.


“Gama an sami mugaye, a cikin jama'ata, Suna kwanto kamar masu kafa ashibta. Sun ɗana tarko su kama mutane.


Bari wannan mutum ya zama kamar biranen da Ubangiji ya kaɓantar ba tausayi. Bari ya ji kuka da safe, Da rana kuma ya ji gangamin yaƙi,


Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Allahna. Ka ji kukana na neman taimako, ya Ubangiji!


Na duba kewaye da ni, sai na ga ba ni da wanda zai taimake ni, Ba wanda zai kiyaye ni, Ba kuwa wanda ya kula da ni.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ