2 “Ka tashi, ka gangara zuwa gidan maginin tukwane, a can zan yi maka magana.”
2 “Ka gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, a can zan ba ka saƙona.”
A zamanin dā, Allah ya yi wa kakannin kakanninmu magana ta hanyoyi masu yawa iri iri, ta bakin annabawa,
Amma ka tashi ka shiga gari, can za a faɗa maka abin da za ka yi.”
Ubangiji kuma ya nuna mini wani wahayi. A wahayin sai na gan shi, yana tsaye kusa da bangon da ake ginawa. Yana riƙe da igiyar awon gini.
Amma da a ce sun tsaya cikin shawarata, Da sun yi shelar maganata ga jama'ata, Da sun juyar da su daga muguwar hanyarsu, Da mugayen ayyukansu.
Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, ya ce, “Tafi ka sayo lilin na yin ɗamara, ka sha ɗamara da shi kada kuwa ka tsoma shi a ruwa.”
A wannan lokaci Ubangiji ya riga ya faɗa wa Ishaya ɗan Amoz, cewa ya tuɓe tsummokin da yake saye da su, ya kuma tuɓe takalmansa. Shi kuwa ya yi biyayya ya yi ta yawo tsirara, ba kuma takalmi a ƙafarsa.
Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce,
Sai na gangara zuwa gidan maginin tukwanen, na iske shi yana ginin tukwane a kan na'urar ginin tukwanen.