Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 18:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Sun mai da ƙasarsu abar banƙyama, Abin raini har abada. Duk wanda ya wuce ta wurin zai razana ya kaɗa kansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Ƙasarsu za tă zama kufai, abin reni har abada; dukan waɗanda suka wuce za su yi mamaki su kaɗa kai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 18:16
35 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Duk wanda ya gan ni Sai yă maishe ni abin dariya, Suna zunɗena da harshensu suna kaɗa kai.


zan aiko kabilai daga arewa da bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Zan kawo su, su yi yaƙi da ƙasan nan da mazaunanta, da dukan al'umman da take kewaya da ita. Zan hallaka su sarai, in sa su zama abin ƙyama, da abin raini, da abin zargi har abada.


Zan mai da wannan birni abin ƙyama, abin raini, dukan wanda ya wuce wurin zai yi mamaki, ya yi tsaki saboda dukan masifun da suka auka wa birnin.


Masu wucewa suka yi ta yi masa baƙar magana, suna kaɗa kai,


Domin kun kiyaye dokokin Omri, Kun bi halin gidan Ahab, Kun kuma bi shawarwarinsu. Domin haka zan maishe ku kufai, In mai da ku abin dariya, Za ku sha raini a wurin mutanena.”


Saboda fushin Ubangiji, ba wanda zai zauna a cikinta, Za ta zama kufai, Duk wanda ya bi ta wajen Babila, zai ji tsoro, Zai kuma yi tsaki saboda lalacewarta.


Gama ni Ubangiji na rantse da zatina, cewa Bozara za ta zama abar tsoro, da abar dariya, da kufai, da abar la'ana. Dukan garuruwanta za su zama kufai har abada.”


Wannan Haikali kuwa zai zama tsibin juji, duk wanda zai wuce ta wurin, zai yi mamaki, ya yi tsaki, ya ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi wa ƙasar nan da Haikalin nan haka?’


Masu wucewa suka yi ta yi masa baƙar magana, suna kaɗa kai, suna cewa, “Ahaf! kai da za ka rushe Haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku,


Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima yana yi maka dariya, kai Sennakerib, yana kuma yi maka ba'a.


Ka faɗa wa mutanen ƙasar, cewa ni Ubangiji Allah na ce mutanen Urushalima da suke a ƙasar Isra'ila za su ci abincinsu da razana, su sha ruwansu da tsoro, gama za a washe dukan abin da yake ƙasarsu saboda hargitsin dukan waɗanda suke zaune cikinta.


Zan nuna ikona a dukan ƙasar, in mai da ita da wuraren zamansu duka hamada. Ƙasarsu za ta zama hamada har zuwa Dibla. Kowa zai sani ni ne Ubangiji’ ”


“Ni Ubangiji na ce, zan mai da Urushalima tsibin kufai, Wurin zaman diloli, Zan kuma mai da biranen Yahuza kufai, inda ba kowa.”


Na yi tambaya na ce, “Har yaushe zai ta zama haka, ya Ubangiji?” Sai ya amsa, ya ce, “Har birane suka zama kufai ba kowa ciki. Har gidaje suka zama kangwaye. Har ƙasar kanta ta zama ba kowa, marar amfani.


Ka maishe mu abin raini a wurin arna, Suna kaɗa mana kai, suna raina mu.


Dukan ƙasa za ta zama kibritu da gishiri, ba shuka, ba amfani, ciyawa kuma ba ta tsirowa, kamar yadda Ubangiji ya kabantar da Saduma da Gwamrata, da Adam da Zeboyim, da zafin fushinsa.


to, Ubangiji zai aukar muku, ku da zuriyarku, da munanan masifu waɗanda ba su kawuwa, da mugayen cuce-cuce marasa warkewa.


Amma za su fita daga ƙasar, ƙasar kuwa za ta ji daɗin hutunta muddin ba su ciki, tana zaman kango. Amma za su tuba saboda sun ƙi kula da ka'idodina, suka yi watsi da dokokina.


Ni zan lalatar da ƙasar har maƙiyanku da suke zaune a ciki za su yi mamaki.


Sa'ad da mutane suka gan ni sun yi mini ba'a, Suna kaɗa kai saboda raini.


“Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa'ad da kuka tafi Masar. Za ku zama najasa, da abin ƙyama, da la'ana, da abin ba'a. Wannan wuri kuwa ba za ku ƙara ganinsa ba.’


Sauran mutanen Yahuza kuwa waɗanda suka ragu, waɗanda suke niyyar zuwa ƙasar Masar da zama, zan sa dukansu su halaka a can. Takobi da yunwa za su kashe dukansu a Masar, da yaro da babba. Za su zama abin la'antawa, da abin tausayi, da abin zargi, da abin kunya.


Kin yi wa mutanen Isra'ila dariya. A kowane lokacin da kika ambaci sunansu, sai ki taɗa kanki da raini kamar an kama su tare da ɓarayi.


Ubangiji ya ce, “Edom za ta lalace, duk wanda ya bi ta wurin zai gigice, ya yi tsaki saboda dukan masifunta.


“Dukanku masu wucewa, ba wani abu ba ne a gare ku? Ku duba, ku gani, ko akwai baƙin ciki irin nawa, Wanda Ubangiji ya ɗora mini, A ranar fushinsa mai zafi.


'Yan kasuwa a cikin al'ummai suna yi miki ba'a, Saboda kin zama musu barazana. Ba za ki ƙara kasancewa ba har abada.’ ”


sai ka yi annabci ka ce, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Da yake sun maishe ku kufai marar amfani, sun kuma murƙushe ku ta kowace fuska, har kun zama abin mallakar sauran al'umma, kun zama abin magana da abin tsegumi ga mutane.


Don haka Ubangiji ya yi fushi da Yahuza da Urushalima, ya sa suka zauna da tsoro, abin banmamaki, abin ba'a kamar yadda kuke gani da idanunku.


Zan fafare su da takobi, da yunwa, da masifa. Zan maishe su abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya. Za su zama abin la'ana, da abin razana, da abin raini, da abin zargi, ga dukan al'ummai, inda na kora su.


Babila za ta zama tarin juji, wurin zaman diloli, Abar ƙyama da abar ba'a, inda ba kowa.


Garuruwanta sun zama abin ƙyama, Ta zama hamada, inda ba ruwa, Ƙasar da ba mazauna, Ba kuma mutumin da zai ratsa ta cikinta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ