Sun birkitar da kome! Wane ne ya fi muhimmanci, mai ginin tukwane ko yumɓun? Abin da mutum ya yi da hannunsa ya iya ce wa mutumin, “Ba kai ka yi ni ba”? Ko kuma zai iya ce masa, “Ai, ba ka san abin da kake yi ba”?
Amma idan ba ku kasa kunne gare ni ba, ba ku kuwa kiyaye ranar Asabar da tsarki ba, kun kuma ɗauki kaya kun shiga ta ƙofofin Urushalima a ranar Asabar, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wuta. Za ta kuwa cinye fādodin Urushalima, ba kuwa za ta kasu ba.’ ”