Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 17:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Gama yana kama da sagagi a hamada, Ba zai ga wani abu mai kyau yana zuwa ba. Zai zauna a busassun wuraren hamada, A ƙasar gishiri, inda ba kowa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango; ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba. Za su zauna a busassun wuraren hamada, a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 17:6
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zai mutu bai ga kogunan man zaitun ba, Ba kuwa zai ga rafuffukan da suke da yalwar albarka ba.


Amma mugaye ba haka suke ba, Su kamar yayi suke wanda iska take kwashewa.


Dukan ƙasa za ta zama kibritu da gishiri, ba shuka, ba amfani, ciyawa kuma ba ta tsirowa, kamar yadda Ubangiji ya kabantar da Saduma da Gwamrata, da Adam da Zeboyim, da zafin fushinsa.


Ku gudu don ku tserar da rayukanku, Ku gudu kamar jakin jeji.


Wanda na ba fili fetal ya zama gidansa, Da ƙasa mai gishiri a wurin zamansa?


Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna Allah na Isra'ila, Na rantse cewa, Mowab za ta zama kamar Saduma, Ammonawa kuma za su zama kamar Gwamrata. Za su zama ƙasar ƙayayuwa Da kwazazzaban gishiri marar amfani har abada. Mutanena waɗanda suka ragu za su washe su, su mallake su.”


Abimelek ya yi yaƙi dukan yini har ya ci birnin, ya kashe mutanen da suke cikinsa. Ya rushe birnin, ya barbaɗe shi da gishiri.


Amma ruwan fadamunsa ba zai yi daɗi ba, za a bar shi a gishirinsa.


Za ku bushe kamar busasshen itacen oak, kamar lambun da ba wanda yake ba shi ruwa.


Shi ne mai yiwuwa ne mugu ya yi girma kamar tsire-tsire, Masu aikata mugayen ayyuka kuma su arzuta, Duk da haka za a hallaka su ɗungum.


Amma dogarin da yake tare da sarki ya ce wa Elisha, “Ko da Ubangiji kansa zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba.” Elisha kuwa ya ce, “Za ka gani da idanunka, zai faru, amma ba za ka ci ba.”


Ya mai da ƙasa mai dausayi ta zama mai gishiri, marar amfani, Saboda muguntar waɗanda suke zaune a can.


saboda haka Ubangiji ya ce, ‘ga shi, zan hukunta Shemaiya, mutumin Nehelam, shi da zuriyarsa ba za a bar masa mai rai ko ɗaya a wannan jama'a ba, wanda zai ga irin alherin da zan yi wa jama'ata, gama ya kuta tayarwa ga Ubangiji,’ ” in ji Ubangiji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ