Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 17:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ku mazauna a tsaunuka da cikin saura, zan ba da dukiyarku da wadatarku ganima saboda dukan zunuban da kuka yi a dukan ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Dutsena a ƙasar da dukiyarku na ƙasar da dukan arzikinku za a ba da su ganima, tare da masujadanku na kan tuddai, saboda zunubi ko’ina a ƙasarku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 17:3
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya ce mini, “Zan ba da wadatarku da dukiyarku ganima kyauta, saboda dukan zunubanku a dukan ƙasar.


“Mika kuwa, mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya faɗa wa dukan mutanen Yahuza cewa, “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce, Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin juji, Ƙwanƙolin dutsen Haikalin zai zama kurmi.’


ya kuma kwashe dukan dukiyar da take cikin Haikalin Ubangiji, da dukiyar da take cikin gidan sarki. Sai ya farfashe tasoshin zinariya da suke cikin Haikalin Ubangiji, waɗanda Sulemanu Sarkin Isra'ila, ya yi. Ya aikata abin da Ubangiji ya riga ya faɗa.


Saboda ku kuwa za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin kufai, Dutse inda Haikali yake zai zama kurmi.


Zan bashe ki a hannun kwartayenki, za su kuwa rushe ɗakunan tsafinki, su tuɓe tufafinki, su kwashe murjaninki, su bar ki tsirara tik.


Ka ce musu, ‘Ya ku duwatsun Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji Allah! Haka Ubangiji Allah ya ce a kan duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka. Ga shi, ni kaina, zan kawo takobi a kanku, zan hallaka wuraren tsafinku.


Maƙiyi ya miƙa hannunsa A kan dukan kayanta masu daraja, Gama ta ga al'ummai sun shiga Haikali, Su waɗanda ka hana su shiga cikin jama'arka.


A kan dukan tsaunukan nan na hamada Masu hallakarwa sun zo, Gama takobin Ubangiji yana ta kisa Daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, Ba mahalukin da yake da salama.


Ba za a gafarta zunuban Isra'ila ba, sai an niƙe duwatsun bagadan arna su zama kamar alli, har kuma ba sauran keɓaɓɓun ginshiƙai ko bagadan ƙona turare.


Zan lalatar da masujadanku, in rurrushe bagaden ƙona turarenku, in jefar da gawawwakinku a kan gumakanku, raina kuwa zai ji ƙyamarku.


Suka sa shi ya yi fushi saboda Masujadansu na arnanci. Suka sa ya ji kishi saboda gumakansu.


Banda haka kuma zan ba da dukan dukiyar wannan birni, da dukan ribarsa, da dukan abubuwa masu tamani, da dukan dukiyar sarakunan Yahuza, ga abokan gābansu, waɗanda za su washe su, su kama su, su kai Babila.


Za a washe dukiyarsu, Za a kuwa rurrushe gidajensu, Ko da yake sun gina gidaje, ba za su zauna a ciki ba, Ko da yake sun dasa inabi, ba za su sha ruwansa ba.”


Ga shi, ina gāba da ku, ya ku mazaunan kwarin, Ya dutsen da yake a fili,’ in ji Ubangiji. ‘Ku da kuke cewa, wa zai iya gangarowa wurinku, Ko kuwa wa zai shiga wurin zamanku?


“Gama ni Ubangiji Allah na ce, a kawo rundunar soja ta yi yaƙi da su, don su firgita su, su washe su.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ