Irmiya 17:26 - Littafi Mai Tsarki26 Mutane za su zo daga biranen Yahuza da wuraren da yake kewaye da Urushalima, daga ƙasar Biliyaminu, da ta Shefela, da ta ƙasar tuddai, da kuma ta Negeb, suna kawo hadayu na ƙonawa da sadakoki, da hadayu na sha, da na turare, za su kuma kawo hadayu na godiya a Haikalin Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202026 Mutane za su zo daga garuruwan Yahuda da ƙauyukan kewaye da Urushalima, daga iyakar Benyamin da gindin tuddan yamma, daga ƙasar tudu da kuma Negeb, suna kawo hadayun ƙonawa da hadayun gari, sadakokin turare da na godiya zuwa gidan Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Za a sayi gonaki da kuɗi, a sa hannu a kan sharuɗa, a hatimce su a gaban shaidu, a ƙasar Biliyaminu da wuraren da suke kewaye da Urushalima, da cikin garuruwan Yahuza, da na garuruwan ƙasar tudu, da a garuruwan kwaruruka, da a garuruwan Negeb, gama zan komar wa mutane da wadatarsu a ƙasarsu, ni Ubangiji na faɗa.”
za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”
Ubangiji ya ce, “Idan kun juyo kuna kiyaye ranar Asabar, kuka daina annashuwarku a tsattsarkar ranata, kuka kuma kira Asabar ranar murna, tsattsarkar rana ta Ubangiji, mai daraja, idan kun girmama ta, har kuka daina bin son zuciyarku, ba ku kuma bar shagulgula su ɗauke hankalinku ba, ko ku hurta maganganun banza,