“Ya Ubangiji, ƙarfina da kagarata, Mafakata a ranar wahala, A gare ka al'ummai za su zo, Daga ƙurewar duniya, su ce, ‘Kakanninmu ba su gāji kome ba, sai ƙarya, Da abubuwan banza marasa amfani.’
Amma zan raira waƙa a kan ikonka, Kowace safiya zan raira waƙa da ƙarfi Ga zancen madawwamiyar ƙaunarka. Kai mafaka ne a gare ni, Wurin ɓuya a kwanakin wahala.
Ya Ubangiji, begen Isra'ila, Duk waɗanda suka rabu da kai, za su sha kunya. Waɗanda suka ba ka baya a duniya za a rubuta su Domin sun rabu da Ubangiji, maɓuɓɓugar ruwan rai.
Ubangiji yana magana da ƙarfi daga Sihiyona, Yana tsawa daga Urushalima, Sammai da duniya sun girgiza. Amma Ubangiji shi ne mafakar jama'arsa, Shi ne kagarar mutanen Isra'ila.