Kukan ce, “Bari Ubangiji ya gaggauta ya aikata abin da ya ce zai yi don mu gani. Bari Allah, Mai Tsarki na Isra'ila, ya i da shirye-shiryensa. Bari mu ga abin da yake nufi.”
Kun gajiyar da Ubangiji Mai Runduna da maganganunku, amma kun ce, “Ƙaƙa muka gajiyar da shi?” Kuna cewa, “Ubangiji yana ganinsu, dukan masu aikata mugunta mutanen kirki ne, yana kuwa ƙaunarsu.” Kuna kuma cewa, “Ina Allah yake wanda yake shi adali ne?”