Irmiya 17:11 - Littafi Mai Tsarki11 “Kamar makwarwar da ta kwanta kan ƙwan da ba ita ta nasa ba, Haka yake ga wanda ya sami dukiyar haram, Yana gaɓar ƙarfinsa, za ta rabu da shi, A ƙarshe zai zama wawa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202011 Kamar makwarwar da ta kwanta a kan ƙwan da ba ita ta zuba ba haka yake da mutumin da ya sami arziki a hanyar da ba daidai ba. A tsakiyar rayuwarsa za su rabu da shi, a ƙarshe kuma zai zama wawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”