Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 16:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Yaro da babba za su mutu a wannan ƙasa, ba za a binne su ba, ba kuwa za a yi baƙin ciki dominsu ba. Ba kuwa wanda zai tsaga jikinsa ko ya aske kansa ƙwal dominsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 “Manya da ƙanana duka za su mutu a wannan ƙasa. Ba za a binne su ba, ba kuwa za a yi makokinsu ba, kuma ba wanda zai tsaga kansa ko ya aske kansa saboda su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 16:6
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ku 'ya'ya ne ga Ubangiji Allahnku, kada ku yi wa jikinku zāne, kada kuma ku yi wa kanku sanƙo saboda wani wanda ya rasu.


Baƙin ciki zalla ya sami Gaza, Ashkelon ta lalace. Ya ƙattin mutane, yaushe za ku daina tsattsage kanku?


sai waɗansu mutane, su tamanin, suka zo daga Shekem, da Shilo, da Samariya, da gemunsu a aske, da tufafinsu a kece, da jikunansu a tsage. Suka kawo hadaya ta gari da hadayar turare domin su miƙa a Haikalin Ubangiji.


ko ku tsattsaga jikinku, ko kuwa ku yi wa kanku jarfa. Ni ne Ubangiji.


Gama kowa ya aske kansa da gemunsa, sun tsattsage hannuwansu. Kowa kuma ya sa rigar makoki.


Ubangiji Mai Runduna yana kiranku ku yi kuka, ku yi makoki, ku aske kawunanku, ku sa tsummoki.


Sai sarakunan duniya, da manyan mutane, da sarakunan yaƙi, da ma'arzuta, da ƙarfafa, da kuma kowane bawa da ɗa, suka ɓuya a kogwanni, da kuma a cikin duwatsu,


za su mutu da muguwar cuta. Ba za a yi makoki dominsu ba, ba kuwa za a binne su ba. Za su zama juji. Takobi da yunwa za su kashe su, gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji.”


Sa'an nan za ka faɗa musu, Ubangiji ya ce, ‘Ga shi, zan sa dukan mazaunan ƙasar su bugu da ruwan inabi, wato sarakunan da suka hau gadon sarautar Dawuda, da firistoci, da annabawa, da dukan mazaunan Urushalima.


“Ku aske gashin kanku, ku zubar da shi. Ku yi makoki a filayen tuddai, gama Ubangiji ya ƙi 'yan zamanin nan, ya rabu da su saboda fushinsa.


Bala'i ɗaya ne zai sami kowa da kowa, firistoci da sauran jama'a, bayi da iyayengijinsu, masu saye da masu sayarwa, masu ba da rance da masu karɓa, attajirai da matalauta.


Sai na ga matattu manya da yara, a tsaitsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Sai kuma aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne Littafin Rai. Aka kuwa yi wa matattu shari'a bisa ga abin da yake a rubuce a cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi.


Sa'ad da Ubangiji ya ba da umarni, babban gida da ƙarami rushewa za su yi.


Da Yesu ya isa gidan shugaban jama'ar, ya kuma ga masu busar sarewa da taro suna ta hayaniya,


Don haka Ubangiji ya bashe su ga Sarkin Kaldiyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a Haikali, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka a hannunsa.


Kada ku yi wa goshinku da gemunku kwakkwafe saboda matattu,


Za a shimfiɗa su a rana, da a farin wata, da a gaban dukan rundunan sama, waɗanda suka ƙaunata, suka bauta wa, waɗanda suka nemi shawararsu, suka yi musu sujada. Ba za a tattara su a binne ba, amma za su zama juji a bisa ƙasa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ