Kuna kuwa ji, kuna gani, ba a nan Afisa kawai ba, kusan ma a duk ƙasar Asiya, Bulus ɗin nan ya rinjayi mutane masu yawan gaske, ya juyar da su, yana cewa, allolin da mutum ya ƙera ba alloli ba ne.
“Don me zan gafarce ki? 'Ya'yanki sun rabu da ni, Sun yi rantsuwa da gumaka, Na ciyar da su har sun ƙoshi sosai, Suka yi karuwanci, suka ɗunguma zuwa gidajen karuwai,
Sarki Nebukadnezzar ya yi gunki na zinariya wanda tsayinsa kamu sittin ne, fāɗinsa kuma kamu shida. Ya kafa shi a filin Dura wanda yake a lardin Babila.
Sun jefar da gumakansu cikin wuta, gama su ba Allah ba ne, amma ayyukan hannuwan mutane ne, waɗanda aka yi da itace da dutse, saboda haka an iya a hallaka su.