don lokaci na zuwa da za su ce, ‘Albarka tā tabbata ga matan da suke bakararru, waɗanda ba su taɓa haihuwa ba, waɗanda kuma ba a taɓa shan mamansu ba.’
Sai Lutu ya fita ya faɗa wa surukansa waɗanda za su auri 'ya'yansa mata, “Tashi, ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma sai surukansa suka aza wasa yake yi.
Ga abin da ni Ubangiji na faɗa a kan 'ya'ya mata da maza da aka haifa a wannan wuri, da kuma a kan iyayensu mata da maza da suka haife su a wannan ƙasa,
Ku auri mata, ku haifi 'ya'ya mata da maza. Ku auro wa 'ya'yanku mata, ku aurar da 'ya'yanku mata, domin su haifi 'ya'ya mata da maza, ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu.
Ka gayyato mini tsoro Kamar yadda akan gayyato taro a ranar idi. A ranar fushin Ubangiji Ba wanda ya tsere, ko wanda ya tsira. 'Ya'yan da na yi renonsu, na goye su, Maƙiyina ya hallaka su.