Irmiya 15:9 - Littafi Mai Tsarki9 Ita wadda ta haifi 'ya'ya bakwai ta yi yaushi ta suma, Ranarta ta faɗi tun lokaci bai yi ba, An kunyatar da ita, an wulakantar da ita. Waɗanda suka ragu daga cikinsu Zan bashe su ga takobi gaban abokan gābansu. Ni Ubangiji na faɗa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Mahaifiya ’ya’ya bakwai za tă suma ta ja numfashinta na ƙarshe. Ranarta zai fāɗi tun lokacin bai yi ba; za tă sha kunya a kuma wulaƙanta ta. Zan sa a kashe raguwa da takobi a gaban abokan gābansu,” in ji Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’